Japan ta bayana janye dakaraun ta daga Irak
June 20, 2006Praministan Japon, Junichiro Koizumi, ya yanke shawara kawo ƙarshen zaman dakarun Japon, a ƙasar Irak.
A wani jawabi da ya gabatar yau ,Praministan ya ce ya ɗauki wannan mataki, bayan dogon nazari, da kuma tantanawa, da ɓangarori daban-daban na ƙasa, da ma gwamnatocin Amurika da na Iraƙin.
Kasar ta aika sojoji 600, tun watan janairu na shekara ta 2004, wanda ke jibge a birnin Samawa na jihar Al Mouthanna.
Praministan Koizumi da zai barin karagar mulki a watan Satumber mai zuwa, ya tabbatar da cewa, Japon zata ci gaba da talafawa Iraƙ, ta wasu hanyoyin na daban.
Ta fannin hare hare kuwa, a yau ma rahotani sun ce a ƙalla, mutane 15 sun rasa rayuka, dukan su yan ta´ada, bayan da sojojin Amurika su ka yi masu luguden wuta.
Sannan kuma, an gano gawawakin sojoji 2, na Amurika, da su ka yi ƙasa ku bisa, tun ranar juma´a da ta wuce.