1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan ta kammala janye sojojinta daga Iraki

July 25, 2006
https://p.dw.com/p/BupG
Ayarin karshe na dakarun da kasar Japan ta girke a Iraqi sun isa gida bayan sun kammala wani aikin soji mafi muhimmnaci da Japan din ta yi tun bayan yakin duniya na biyu. Dakarun su kimanin 600 sun gudanar da aikin jin kai a birnin Samawa dake kudancin Iraqi. Ba su shiga cikin rigingimun da ake yi a kasar ba. A wani lokaci yau ne kuma FM Iraqi Nuri al-Maliki zai gana da shugaba GWB na Amirka a birnin Washington. A lokacin da ya yada zango a birnin London, Maliki ya nunar da cewa a kowace ranar Allah ta-ala ana halaka fararen hula kimanin 100 a fadin kasar ta Iraqi. Ya kuma tabbatar da rahoton da MDD ta bayar cewa fararen hula dubu 5 da 818 aka kashe a Iraqi a cikin watannin mayu da yuni.