Japan ta shirya dawo da jiragen ruwanta daga Afghanistan
November 1, 2007Kasar Japan ta shirya dawo da jiragen ruwanta da suke marawa Amurka baya a Afghanistanbayan gwamnatin kasar ta gagara cimma matsaya kann kara waadin jamianta a Afghanistan.Wani mai magana da yawun gwamnatin Japan ya sanarda haka wajen wani taro da manema labarai a birnin Tokyo.manyan jiragen ruwa na Japan dake kann tekun Indiya suna bada mai ne ga dakarun Amurka da na sauran kasashe dake aiki a Afghansitan karkashin dokar data amincewa kasar taimakawa Amurka yaki da taaddanci.A kuma yau ne wannan doka take kammala aikinta haka kuma abokan adawa wadanda suke rike da majalisar dattajai sun toshe duk wani kokari da akeyi na kara waadin wannan doka.A halinda ake ciki kuma rahotanni sunce an kashe wasu yan kungiyar Taliban kusan 59 cikin wani hari da dakarun NATO suka kai a birnin Kandahar.