1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan tace zata dakatar da taimako ga hukumar Palasdinawa

April 18, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1a

Kasar Japan tace zata dakatar da bada taimako ga hukumar Palasdinawa,har sai kungiyar Hamas ta baiyana kudirinta na bin kaidojin yarjejeniyar zaman lafiya na yankin gabas ta tsakiya.

Japan din wadda ta bada taimakon dala miliyan 840 ga hukumar ta Palasdinawa tun daga 1993,tace zata ci gaba da bada taimakon jin kai idan bukatar hakan ta taso.

Mataimakin sakataren yada labarai na maaikatar harkokin wajen Japan,Akira Chiba yace,kasarsa ta shirya bada kayayiyakin abinci da kudinsu ya kai dala miliyan 6 ga hukumar Palasdinawa amma ta hanyar wata kungiyar agaji ta kasa da kasa,ba kai tsaye ga kungiyar Hamas ba.