1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan zata baiwa kasashe masu tasowa dala biliyan 10

December 9, 2005
https://p.dw.com/p/BvHF

Shugaba Junichiro Koizumi na kasar Japan yace, Japan zata baiwa kasashe masu tasowa,taimakon kudi dala biliyan 10,cikin wani shirinta na shekaru uku domin habaka harkokin kasuwanci tsakaninta da kasashen,a kokarinsa na samun goyon baya kafin babban taron kungiyar ciniki ta duniya da zaa bude a mako mai zuwa a Hong Kong..

Kozumi yayi wannan sanarwar ce a lokacin wata ganawarsa da jakadu 39 na wasu kasashe masu tasowa.

Kanfanin dillancin labarai na Kyodo,ya ruwaito cewa,wannan taimako yana wani bangare ne na aniyar Japan ta karfafawa kasashe masu tasowa gwiwa wajen taron na kungiyar ciniki ta duniya.