1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Harin ta'addanci a birnin Ouagadougou

Mohammad Nasiru AwalJanuary 22, 2016

Harin ta'addancin da aka kai a babban birnin kasar Burkina Faso na zama kalubale ga sabon shugaban kasa Roch Marc Kabore.

https://p.dw.com/p/1HiQ6
Burkina Faso, Soldaten nach Terroranschlag
Hoto: Reuters/J. Penney

A labarin da ta buga mai taken birnin Ouagadougou ya kadu, hari a Burkina Faso, kalubale ga sabon shugaban kasa Roch Marc Christian Kabore jaridar Neues Deutschland cewa ta yi:

"Kasar Burkina Fasso ba ta taba fuskantar mummunan hari irin na ranar Jumma'a da ya halaka mutane kimanin 30 a birnin Ouagadougou ba. Shi ne kuma hari mafi muni cikin lokaci mai tsawo a yankin Yammacin Afirka wanda kuma ya auku a tsakiyar babban birnin da kawo yanzu yake da cikakken tsaro kuma ke maraba da baki. Yanzu dai kamar makwabciyarta Mali, dole ne Burkina Faso ta kwana da sanin fuskantar barazanar hare-haren ta'addanci. Sai dai muhimmin abu a matakin farko shi ne yadda shugaba Roch Marc Kabore zai tinkari wannan sabon kalubale.

Hada karfi don yaki da tarzoma

Afirka ta Yamma na neman dubarun yaki da ta'adda inji jaridar Die Tageszeitung a labarin da ta buga game da harin na birnin Ouagadougou.

Burkina Faso Anschlag auf Splendid Hotel in Ouagadougou Modibo Keita
Firaministan Mali Modibo Keita (tsakiya) da takwaransa na Burkina Faso Paul Kaba Thieba (hagu)Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Ta ce tun bayan harin ta'addanci a babban birnin Burkina Faso, Ouagadougou, kasashen yammacin Afirka ke kokarin yin aiki tare da nufin ganin hare-hare na ta'addanci da ke kokarin gagarar kundila a yammacin Afirka ya zama tarihi. Tuni dai Firaministan Mali Modibo Keita da shugaban Jamhuriyar Benin Boni Yayi da ke zama shugaban kungiyar ECOWAS suka kai ziyara Ouagadougou a wani yunkuri na samun nagartattun hanyoyin yaki da kungiyoyin tarzoma a yankin na yammacin Afirka.

Barazanar matsalar yunwa a sassan Afirka

To daga batun tarzoma sai matsalar kamfar ruwa da fari a wasu sassa na nahiyar Afirka.

A sharhin da ta yi jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce yanayin zafin nan da ake wa lakabi da "El Nino" ya yi tsanani musamman a kudanci da kuma gabashin nahiyar Afirka, kuma yanzu haka sama da mutane miliyan 20 na neman taimako sakamakon rashin damina mai kyau saboda kamfar ruwa da yanayin zafin ya janyo.

El Nino Kolumbien Dürre
Kamfar ruwa saboda yanayin El NinoHoto: Getty Images/E. Abramovich

Jaridar ta rawaito hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya na cewa yanzu haka mutane miliyan 14 a kudancin Afirka ke fuskantar barazanar matsananciyar yunwa. Ta ce halin da ake ciki yayi muni a kasar Habasha da ke can yankin kahon Afirka inda ake fama da fari. Jaridar ta ce a bana mutane kimanin miliyan 10 a kasar ta Habasha za su dogara kan taimakon abinci daga ketare.

Ci da gumin yara a aikin hakar ma'adanai

Kwadagon yara don wayoyin salula na Smartphones har wayau dai inji jaridar ta Süddeutsche Zeitung tana mai nuni da sukar da kungiyar Amnesty International ta yi kan yadda ake amfani da yara wajen aikin hakar ma'adanan Cobalt a kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango. Ta ce karfen na Cobalt na daga cikin karafa masu daraja da ake amfani da su wajen kera wayoyin salula na zamani, amma ana ci da gumin kananan yara wajen hakan wannan ma'adanan.