1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janye sojojin Faransa a Mali cikin jaridun Jamus

Abdullahi Tanko Bala LMJ
February 18, 2022

Galibin jaridun na Jamus din, a wannan makon sun mayar da hankali ne a kan janyewar sojojin Faransa a Mali da kuma yan ta'adda da suka addabi kasar ta Mali.

https://p.dw.com/p/47GBA
Afirka I Sojoji I Rundunar Barkhane a Mali
Takaddama tsakanin Mali da uwar gijiyarta Faransan ce ta sa Faransa kwashe sojojintaHoto: Etat-major des armées / France

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi tsokaci da cewa manufar janye sojojin Faransa a Mali shi ne domin matsa lamba a kan gwamnatin mulkin soja a Bamako, to sai dai matakin ya bar wagegen gibi. Jaridar ta ce kawo karshen zaman sojojin Faransa a Mali, zai yi tasiri a kan aikin sojojin Jamus a yankin Sahel. Ta ce Faransa za ta janye rundunar sojanta ta Barkhane a daidai lokacin da take tsakiyar yaki da masu tayar da kayar baya musamman a shekarun baya-bayan nan. Sai dai kuma sauran rundunonin kwantar da tarzoma kamar sojojin kungiyar Tarayyar Turai da ke taimakawa wajen bayar da horo da kuma sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA, za su ci gaba da kasancewa a Malin a halin yanzu.

A nata bangaren Jaridar Die Welt a sharhinta mai taken Faransa ta tafi amma 'yan ta'adda na nan, ta ce Faransa za ta janye daga Mali amma ba a gama da yaki da 'yan ta'adda a yankin Sahel ba. Jaridar ta ce Mali ba Afghanistan ba ce, wannan shi ne sakon da Faransa ta ke son isarwa kafin ta janye daga Mali. Ba za ka so ka zama kasasshe ba kuma ba zai yi wu a yi watsi da rayuwar fararen hula ba, a cewar shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Ita kuwa jaridar die Tageszeitung ta yi sharhi ne kan taron koli tsakanin kungiyar Tarayyar Turai da Afirka, inda ta tabo dangantaka tsakanin nahiyoyin biyu da kuma batun annobar corona. Jaridar ta ce annobar corona ta kawo rauni sosai a dangantakar da ke tsakanin EU da Afirka. Sai dai kuma kungiyar Tarayyar Turan na fatan kara yin hobbasa wajen zuba jari a Afirkan, domin cimma tasirin Chaina a nahiyar. Taron karshe da aka yi tsakanin EU da Afirka shi ne a 2017 a birnin Abidjan, wanda kuma aka tashi ba tare da cimma wata matsaya ba. An sami bambance-bambance masu yawa, misali kan batun 'yan gudun hijira. Ana tsaka da haka sai ga corona ta zo ta kara dagula dangantaka a tsakanin nahiyoyin biyu. To amma wasu na cewa taron da aka yi a tsakanin nahiyoyin biyu a wannan makon, wata babbar nasara ce.

Taron Afirka da EU | Beljiyam Brüsse
Taro karo na farko na Afirka da Tarayyar Turai, tun bayan barkewar annobar coronaHoto: Dursun Aydemir/Anadolu Agency/picture alliance

Ursula von der Leyen shugabar Hukumar Tarayyar Turan ta ce, EU za ta tallafawa Afirka da allurai miliyan 440 da kuma kudi Euro biliyan daya domin kafa cibiyar yin magunguna. Sai dai kuma kungiyar Tarayyar Afirka ta ce ba a nan gizo ke sakar ba, abin da ta ke bukata shi ne dage hakkin mallaka kan fasahar hada magungunan wanda haka ne zai bai wa nahiyar Afirka damar iya samar da magungunan cikin sauki domin tunkarar duk wata annoba a nan gaba. Kawo yanzu dai kashi goma 11 ne kacal cikin 100 na al'ummar Afirka aka yi wa allurar riga-kafin corona, yayin da kasashen nahiyar turai suka yiwa kashi 72 cikin 100 na al'ummarsu riga-kafin a cewar shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa.