1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jerin sunayen membobin majalisar ministocin Najeriya

Mohammad Nasiru AwalOctober 9, 2015

Majalisar ministocin Najeriya da halin da ake ciki a Burkina Faso na daga cikin batutuwan Afirka da jaridun Jamus suka yi sharhi kansu.

https://p.dw.com/p/1GlvQ
Präsident von Nigeria Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Bari mu fara sharhunan jaridun na Jamus game da nahiyarmu ta Afirka da jaridar Die Tageszeitung wadda ta buga labari game da kashin fako na jerin sunayen ministocin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika wa majalisar dattawan kasar.

Ta ce sabbin fuskoki a cikin gwamnati, bayan watanni hudu da kama madafun iko shugaba Buhari na Najeriya ya gabatar da sunayen mutane 21, uku daga ciki mata da yake son ba su mukaman ministoci a gwamnatinsa. Jaridar ta ce yanzu haka batun da ya fi daukar hankali Najeriya kasar da ta fi yawan al'umma a Afirka, shi ne na ministocin. Sunayen tsoffin gwamnoni a jerin wato Kayode Fayemi da Rotimi Amaechi da kuma Babatunde Fashola ba su zo da mamaki ba. Ana yi wa wadannan mutane dai shaidar wadanda suka yi wa jihohinsu ayyuka na gari. To sai dai kuma matasa ba su samu gurbi a jerin sunayen ministocin ba. Buharin ma mata uku kadai ya nada ciki akwai Amina Mohammed da tun a shekarar 2012 take wa Majalisar Dinkin Duniya aiki a matsayin mai ba wa babban sakataren majalisar Ban Ki-Moon shawara kan matakan da za su biyo bayan muradun karni a bana.

Jagororin juyin mulkin sun shiga hannu

An kame jagoran juyin mulkin kasar Burkina Faso bayan da ofishin jakadancin fadar Vatikan a birnin Ouagadougou ya mika shi ga hukumomin kasar, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung.

Burkina Faso Ouagadougou General Gilbert Diendere
Janar Gilbert Diendere na fuskantar tuhumar cin amanar kasaHoto: picture alliance/Photoshot

Ta ce bayan da Janar Gilbert Diendere da tsohon ministan harkokin waje karkashin tsohuwar gwamnatin Shugaba Blaise Compaore, wato Bassole sun shiga hannu yanzu an dukufa wajen neman sauran mutanen da suka taka rawa a juyin mulkin da bai dore ba a Burkina Faso. Ana zargin mutanen da kokarin hana a kwance damarar rundunar sojin RSP da ke gadin fadar shugaban kasa. Ana kuma zarginsu da neman taimako daga sojojin ketare. A zaman farko da ta yi bayan yamutsin a fadar shugaban kasa, majalisar ministoci ta zartas da hukuncin kwance damarar yakin rundunar RSP. Gwamnatin rikon kwaryar kasar dai ta yi alkawarin mutunta hakkin wadanda aka kamen.

Fadi ba cikawa daga hukumomin lamuni

Alal hakika kamata ya yi Bankin Duniya ya taimaka wa matalauta, amma ana tilasta wa miliyoyin mutane tashi daga yankunansu saboda da ayyukan da Bankin bai da da kudaden gudanarwa, inji jaridar Süddeutsche Zeitung sannan sai ta ci gaba kamar haka:

Chancella Damzousse Bangui
Tada mutane daga yankunansu na asali saboda aikin raya kasaHoto: DW/Scholz/Kriesch

Ko da yake Bankin Duniyar ya sha daukar alkawuran ba da karin kariya ga mutanen da ke rasa muhallinsu sakamakon aikace-aikacen da kafofin lamuni na duniya ke ba da kudin aiwatarwa, amma kawo yanzu shiru kake ji kamar an shuka dusa. Amma halin da ake ciki wani Fasto dan kasar Habasha Omot Agwa ya shiga hannun hukumomin kasar saboda yakin da yake yi da irin cin zarfin da ake wa kabilar Anuak da akasarinsu Kirstoci ne a Sudan ta Kudu da kuma yammacin kasar Habasha. Shi dai Faston ya yi wa wani kwamitin bincike na Bankin Duniya aikin matsayin tafinta. Kwamitin dai na son ya gano gaskiyar zargin da ake wa hukumomin Habasha da lafin amfani da kundin Bankin Duniya suna korar al'ummar ta Anuak daga yankinsu na asali.