1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta katse jiragenta zuwa Kanada

Abdul-raheem Hassan
August 7, 2018

Bayan da Saudiyya ta kori jakadan Kanada tare da dawo da jakadanta ta kuma katse huldar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, yanzu ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/32j4f

Rikicin dipolomasiyya da ke tsakanin masarautar Saudiyya da kasar Kanada, na ci gaba da ruruwa, inda a baya-bayannan kamfanin jiragen saman Saudiyyan ya sanar da dakatar zirga-zirgar dukkannin jiragenta zuwa Toronto.

Makasudin daukar wadannan matakan dai, shi ne suka da Kanada ta yi kan sabon yunkurin kama mata da 'yan gwagwarmayar kare hakkin dan Adam a Saudiyya.  Abin da Saudiyyar ta kira "shisshigi da neman wuce makadi da rawa" a harkokin cikin gida.