Jirgin kasa daga Addis Ababa zuwa Djibouti
Daga farkon shekarar 2018 wani jirgin kasa da wani kamfanin China ya samar ya fara jigilar mutane da hajojinsu daga Habasha zuwa tashar jiragen ruwa ta Djibouti.
Hadin gwiwar China da Habasha da Djibouti
Wannan tashar jirgin ita ce dan ba ta layin dogo daga Addis Ababa zuwa Djibouti wanda aka fara amfani da shi a watan Janairun 2018. Wannan wani hadin gwiwa ne tsakanin hukumar jiragen kasa ta Habasha da ta Djbouti da kuma ta China. Gwamnatin China ce ta jagoranci wannan aiki wanda aka kashe Dala biliyan 4.
Dokoki da Ka'idoji
Jami'an tsaro Ethiopian Habasha da ke tsaron tashoshin jiragen kasa kan marabi fasinjojin da ke son zuwa Djibouti da karfe 8 na safe. 'Yan China ne ke tafiyar da harkokin jirgin kasan kuma za su ci gaba da yin hakan har tsawon shekaru 6. Ma'aikatn jirgin yanzu haka 'yan China ne haka ma abin ya ke ga masu gyaransa.
Hanyar fita daga gari
Hanyar da aka shimfida layin dogo a wajen garin Addis Ababa na kasar Habasha na cike da kauyuka da gonaki sannan a kan yi kiwon shanu a yankin. Wannan ne ma ya sanya matuka jiragen kasan kan tafi a hankali a irin wadannan wuraren kamar yadda manajan da ke kula da jiragen Wang Hugue ya nunar. Kamfanin jirgin kasan kan biya diyya ga masu shanun da jirgi ya kadewa dabbobinsu.
Tafiya cikin jin dadi
Yin tafiya a mota na da wuyar gaske don dole ne wani lokacin a sauya mota ko ma ka kwana a kan hanya. Mutum kan shafe kwana guda da yini daga Addis Ababa zuwa Djibouti in ji Linda, wata malamar makaranta da ke koyar da Ingilishi. Yanzu ana yin awa 12 daga Habasha zuwa Djibouti a jirgin kasa amma duk da haka tafiyar ta fi dadi.
Yin lalle yayin da ake kan hanya
Ba kasafai jirgin kan cika da fasinjoji ba, wannan ya sanya mutane ke da damar yin abubuwa da yawa ciki kuwa har da yin lalle yayin da suke kan hanya. Jirgin ya fi mayar da hankalinsa ne kan kayan da yake dauko ba wai yawan fasinja ba don tarogon fasinja hudu ne amma na kaya musamman ma wanda ake bukata a Habasha sun kai 106.
Samun karin fasinja
A kan samu karin fasinja da zarar jirgin ya ci rabin zango na tafiyar da zai yi mai nisa kilomita 728. Jirgin kan cika da hirarraki ta fasinjoji da ke magana cikin harsunan da suka hada da Amharic da Somali da kuma Faransanci. Mutane kan kasance cikin raha inda sukan yi wa juna kyautar abinci. Kade-kaden da ake sanyawa a wannan lokaci kan kara armashin tafiyar.
Amfani da tabar nan ta Khat
Lokacin da tafiya ta mika, fasinjoji kan yi amfani da tabar nan ta Khat wadda ake ci a kasashen da ke yankin kusurwar Afirka. Wannan lamari bai kwanta wa masu lura da jirgin ba don an haramta amfani da ita a China amma in ji manajan jirgin wato Mr. Hugue ''daga baya mun saba''. Hugue ya ce da an haramta amfani da ita a jirgin amma daga bisani aka kyale su tunda al'adarsu ce.
Kan tafarki na gari
Masu sharhi kan lamuran siyasa suka ce jigilar fasinjoji da kaya da ake tsakanin Djibouti da Habasha ba tare da shinge ko fuskantar wata matsala ba alama ce ta wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashen da ke kusurwar Afirka.