Jirgin soji mai saukar ungulu ya rikito a Nijar
December 26, 2022Talla
Sanarwa ta ce wani jirgin sama mai saukar ungulu kirar MI-17 na rundunar sojan Nijar, da ya dawo daga wani atisayen da ya saba yi, nya yi hatsari a lokacin da yake sauka a filin saukar jiragen sama na soja na Yamai. Mutanen guda uku da suka mutu wadanda suka hada da wasu hafsoshin sojojin Nijar biyu da wani malami dan kasar waje sun mutu nan take duk da kokarin da hukumar agajin gaggawa ta yi na shawo kan gobarar da ta tashi a cikin jirgin. Gwamnatin Nijar ta ce za ta gudanar da bincike domin sanin musabbin hatsarin.