1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

John Kerry na ziyarar bazata a Somaliya

Yusuf BalaMay 5, 2015

Wannan ziyara ta John Kerry ta kasance ta farko da wani sakataren harkokin wajen kasar ta Amirka ke yinta a wannan kasa ta Somaliya da yaki ya daidaita.

https://p.dw.com/p/1FKLF
Lausanne Atomverhandlungen Abschlußstatement Kerry
Hoto: Reuters/Ruben Sprich

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry na wata ziyarar ba zata a kasar Somaliya a yau Talata, abin da ya sanya ya kasance sakataren harkokin wajen kasar ta Amirka na farko da ya ziyarci wannann kasa da yaki ya daidaita.

Babban jami'in difolomasiyar ta Amirka ya tsara tsayawa a birnin Magadishu fadar gwamnatin kasar ta Somaliya a ranar talata, sai dai ba zai bar harabar filin tashi da saukar jiragen saman birnin ba inda zai gana da shugaba Hassan Sheikh Mohamud da firaminista Omar Abdirashid Ali Sharmake.

Ziyarar ta sakatare Kerry an tsarata ne da nufin kara inganta dangantaka da ke tsakanin kasar ta Amirka da mahukuntan kasar ta Somaliya da ke samun goyon bayan kasar ta Amirka musamman a fafutikar da suke yi wajen yaki da kungiyar Al'kaida reshen Somaliya.