Kabore ne sabon shugaban Burkina Faso
December 1, 2015Talla
Mr. Kabore dai ya samu kashi 53.4 cikin 100 na kuri'un da aka kada yayin da babban mai hammaya da shi Zephirin Diabre ya samu kashi 29.3, batun da ke nuna cewar ba sai an yi zagaye na biyu a zaben ba. Tuni ma dai Mr. Diabre ya taya abokin takararsa murar lashe zaben.
Da ya ke jawabi gaban dubban magoya bayansa, Roch Marc Christian Kabore ya ce lokaci ya yi da za su dukufa wajen ganin fara aiki domin sake gina kasar domin amfanar al'ummar Burkina Faso. Al'ummar kasar kimanin miliyan 18 dai yanzu haka na fata na ganin sauyi bayan da a baya ta sha fama da tsoma bakin sojin wajen tafiyar da ita da kuma mulki irin na mahadi ka ture.