1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kabore ne sabon shugaban Burkina Faso

Salissou BoukariDecember 1, 2015

Hukumar zaben kasar Burkina Faso CENI ta ce tsofon Firaminista Rock Mark Christian Kabore ya lashe 53,49% na kuri, saboda haka ya zama zababben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/1HFIm
Burkina Faso Wahl in Ouagadougou Präsdentschaftskandidat Roch Marc Kabore
Hoto: Reuters/J. Penney

Kabore ne sabon shugaban Burkina Faso

Rock Mark Christian Kabore ya taba zama Firaminista a lokacin mulkin shugaba Blaise Compaore. Nasarar da ya samu a zaben za ta kasance wani mataki na kawo canji a Burkina Faso, wacce dukkannin shugabanninta suka hau kan karaga ta hanyar juyin mulki tun lokacin da kasar ta samu mulkin kanta a shekara ta 1960.

Zaben shugaban kasar da aka gudanar na 'yan majalisun dokoki da na shugaban kasa, zai kawo karshen mulkin gwamnatin rikon kwarya da aka kafa a kasar ta Burkina Faso tun bayan murabus din da shugaba Compaore ya yi ta dalilin matsin lamba daga 'yan kasar.

Burkina Faso Präsidentschaftswahlen Zephirin Diabre
Sauran 'yan takara su taya Kabore murnaHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo/picture alliance/AA/Olympia de Maismont

Tuni dai sabon shugaban kasar Rock Mark Christian Kabore ya yi jawabinsa na fako a gaban dubunnan magoya bayansa da ke cike da murnar wannan nasara. Ya ja hankali kan wajibcin " hada karfi da karfe domin mantawa da duk wasu miyagun abubuwa da suka faru, don samun nasara cikin yanayi na gaskiya da shari'a ta hada kan 'yan kasa da kuma karfafa dankon zumunci da zaman tare tsakanin dukannin 'yan Burkina Faso."

Shi dai zababben shugaban kasa Mark Christian Kabore, bayan mukamin Firaminista, ya taba rike mukamin shugaban majalisar dokokin Burkina Faso a lokacin mulkin shugaba Compaore kafin daga bisani su raba gari, inda ya kafa tashi jam'iyyar a shekara ta 2014.

Burkina Faso Präsidentschaftswahl - Gewinner Roch Kaboré
Kabore ya nemi a hada kai a Burkina FasoHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Kabore ya samu karbuwa da tazara mai yawa a gaban abokan hamayyarsa guda 13 wanda na kusa da shi shi ne Zephirin Diabre wanda ya samu kashi 29,7% na yawan kuri'un da aka kada. Sai dai shi wanda ya zo na biyun ya nuna dattaku inda tun da wuri ya isar da gaisuwar taya murna ga sabon shugaban kasar ta hanyar zuwa da kanshi

Diabre ya ce ya " dauri aniyar mika gaisuwaa ta taya murna zuwa gareshi (Kabore) domin ga dukkan alamu shi ne zai kasance sabon shugaban kasarmu Burkina Faso, ta sabili da haka ne tare da rakiyar mutanena na isa a can cibiyar magoya bayansa domin sanar da shi wannan aniya tawa."

Kashi 60% na wadanda suka yi rejista ne suka samu fita domin kada kuri'un nasu a wannan zabe mai cike da tarihi, wanda ya gudana cikin nitsuwa da kwanciyar hankali. Wannan ya nunar a fili gogewar da 'yan Burkina Faso suka yi a fannin son kasa da neman zaman lafiya a cewar shugaban hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta CENI Barthelemy Kere:

Yayin wani taron manema Labarai, Mista Kere ya ce " Ina mai isar da gaisuwar taya murna na farko ga shi wanda ya yi nasara wanda kuma yake da 'yancin nuna farincikinsa ganin yadda mutane suka zabeshi don ya jagorancin wannan kasa. Sannan ina mai taya murna ga dukannin 'yan takara da suka fafata a wannan zabe domin nasara tasu ce ta su duka, kuma sun yi yakin neman zabe cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, sannan da yarda da kaddara."

Burkina Faso Wahl in Ouagadougou
Fiye da wadanda suka yi rejista sun kada kuri'a a Burkina FasoHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Kafin wannan zabe dai, an fuskanci tarin matsaloli a Burkina Faso inda Sojojin da ke tsaron fadar tsofon shugaban kasar na RSP, suka aiwatar da wani juyin mulki ga hukumomin rikon kwaryar, kafin daga bisani su mika wannan mulki da kansu ta sabili da matsin da suka fuskanta a ciki da wajen kasar.

Tuni dai Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yaba yadda zaben kasar ta Burkina Faso ya gudana.