Kafando: Zabe, nasara ce ga Burkina Faso
November 29, 2015A lokacin da ya yi wajabi bayan da ya kada kuri'arsa Michel Kafando ya ce gwamnatinsa ta cika alkawarinta na gudanar da zabe shekara guda bayan fara rikon kwarya. Tun a ranar 11 ga watan Oktoban da ya gabata ne dai aka so shirya wannan zabe, amma aka dageshi bayan komabayan da aka samu a sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 17 ga watan Satumba kafin su sake mika mulki ga gwamnatin rikon kwarya a bisa matsin lambar kasashen duniya.
Mutane kimanin miliyan biyar da rabi ne daga cikin kusan miliyan 20 da kasar ta kunsa suka cancanci kada kuri'ar a wannan zabe mai cike da tarihi da ya kasance na farko da kasar ta shirya domin zaben wani shugaba farar hula a karkashin tsarin demokaradiyya:
Wata mace da ta kada kuri'a ta ce "mu abin da muke jira daga sabon shugaban shi ne ya maida hankali kan matsalar mata da ta ilimi da kuma aiki."
'Yan takara 14 ne suka fafata a zaben shugabancin kasar a wa'adin mulki na shekaru biyar.