Ayyukan kungiyoyin 'yan ta'adda a Jamhuriyar Nijar, na ci gaba da yin barazana ga makomar ilimi a wasu yankunan kasar. Matsalar rashin tsaron dai ta tilasta rufe makarantu a wasu kauyukan, tare da kwaso daliban zuwa wasu manyan garuruwa. Sai dai daliban kauyuka da dama sun dakatar da zuwa makarantar baki daya.