1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen tattalin arziki ga ECOWAS

Abdourahamane Hassane
January 31, 2024

Kwararu da masana na ci gaba da yin gargadin cewar janyerwar kasashen Mali da Burkina da Nijar daga kungiyar ECOWAS zai yi matuktar dagula tattalin arzikin yankin yammacin Afirka.

https://p.dw.com/p/4bsrd
Taron shugabannin ECOWAS a Abuja, Najeriya
Taron shugabannin ECOWAS a Abuja, NajeriyaHoto: Kola Sulaimon/AFP

Kasar Senegal ala misali ta dogara ne kan shigo da dabbobi da kankana daga kasar Mali don wadata Dakar da kasuwannin da ke kewaye da ita. Har ila yau tashar jiragen ruwa ta Dakar ta dogara ne ga fiye da kashi 50% na kayayyakin da ake shigowa da su daga Mali, a cewar alkaluman hukumar kididdiga ta kasa a shekarar 2022. To amma bangaran huldar tattalin arziki tsakanin Najeriya da Nijar Abubakar Issufu Kado wani masannin tattalin arziki ya ce Najeriya za ta yi asara amma a bangaran gwamnati kawai, ba cundaya tsakanin al'ummomin kasashen ba.

Karin Bayani: Nijar: ECOWAS za ta tattauna da sojoji

Idan har ba a daidaita ba tsakanin wadannan kasahe guda uku da ECOWAS tabbas komai dadewa sai wadannan kasashe sun canza takardar kudinsu. Shin yaya karfin sabbin kudaden kasahen zai iya kasancewa a kasuwannni hada hada na duniya?

Karin Bayani: ECOWAS za ta yi taro kan matsalolin juyin mulkin sojoji a yankin

ECOWAS dai ta ce tana ci gaba da tattaunawa da kasahen domin hana su ficewa saboda hakan zai iya haddasa rauni ga tattalin arzikin yankin yammacin Afirka.

Shugabannin na kasashen yankin Sahel dai na ci gaba da daukar dokoki ba tare da wani fargaba ba wanda ya sa ake yi musu kallon wani sabon yunkuri na juyin juya hali wadanda ba su tsoron ta kife game da irin matakan da suke dauka a gaban ko wacce kasa komai karfinta kuma komai girmanta