1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon babi a rikicin Amurka da China

Zainab Mohammed Abubakar
March 7, 2019

Katafaren kamfanin latroni na kasar China watau Huawei, ya gurfanar da gwamnatin Amurka gaban kotu, bisa zargin takaita harkokin kasuwancinsa a kasar wanda ya sabawa tsarin doka

https://p.dw.com/p/3Ea0s
Huawei
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/A. Wong

Kamfanin ya sanar da shigar da koken nasa a gaban babban kotun tarayya da ke Texas, tare da kalubalantar sashi na 889 na dokar tsaron Amurkan, wanda ke haramtawa dukkan ma'aikatu da 'yan kwangilarsu sayen dukkan kayan da Huawei ya sarrafa, dokar da shugaba Donald Trump ya rattaba hannu a kai a watan Augusta.

Karar da kamfanin na Huawei ya shigar dai na mai zama sabon babi a rikicin da ke tsakanin kasashen na China da Amurka na baya bayannan, wadanda suka yi ta dorawa juna harajin biliyoyin daloli akan hajojin da kasashen biyu ke kasuwancinsu a shekarar da ta gabata.

An dai kai kammala shekarar ta 2018 da capke babban jami'in da ke kula da harkokin kudi na Huawei a Canada, bisa umurnin Amurka.