Kamfanin Huawei ya yi watsi da zargin Amirka
January 29, 2019Talla
Fitaccen kamfanin kera wayoyin salula na kasar China Huawei, ya zargi Amirka da yi masa karya na saba dokokin kasuwanci da aikata zamba a harkokin kasuwancin da ya ke yi a Amirka. Ma'aikatar shari'a ta Amirka ta ce kamfanin Huawei na satar bayanan fasaha da leken asirin kasuwanci, tare da yi wa bankunan Amirka karya. Katafaren kamfanin sadarwar Huawei ta zargi hukumomin Amirka da yin watsi da bukatar tattauna batun tsare wata babbar jami'ar kamfanin da aka tsare a kasar Kanada a shekarar 2018.