1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin arzikin kamfanonin kera makamai na bunkasa

Mouhamadou Awal Balarabe RGB
December 6, 2021

Wani sabon rahoto ya baiyana yadda wasu manyan kamfanonin kera makamai a duniya ke ci gaba da samun gwaggwabar riba a daidai lokacin da duniya ke tsaka da annobar corona.

https://p.dw.com/p/43tkI
Russisches Raketenabwehrsystem S-400
Hoto: picture-alliance/dpa/V. Sharifulin

Wani sabon rahoto da cibiyar binciken zaman lafiya ta SIPRI ta fitar ya nuna cewa manyan kamfanonin kera makamai guda 100 a duniya sun ci gaba da habbaka  cinikinsu  a cikin shekarar 2020 a daidai lokacin da ake tsaka da annobar corona. Wadannan kamfanoni sun yi cinikin miliyan duba 531 duk da masassara da tattalin arzikin duniya ta fuskanta a baya-bayannan.

 Annobar corona ta haifar da durkushewar tattalin arziki a duniya sakamakon matakan kulle da rashin wadatar ma'adinan kere-kere da kuma rauni saye da sayarwa. Sai dai masana'antar kera  makamai ba ta ji radadin wannan koma baya ba ko kadan ba. Maimakon haka ma wani sabon rahoto da cibiyar binciken zaman lafiya ta Stockholm SIPRI ta fitar kan manyan kamfanonin kera makamai 100 na duniya ya tabbatar da cewa sun samu ci-gaba ainun.

Infografik SIPRI Top 6 Export Countries EN
SIPRI ta nuna kasashen da suka fi cinikin makamai a duniya

Miliyan dubu 531 na dalar  Amirka  wadannan manyan kamfanonin dari da suka shigar lalitarsu bayan sayar da makamai a shekarar 2020. Hasali ma wannan kudin ya fi karfin habakan arzikin kasar Beljiyam. Kuma ba tare da mamaki ba, kamfanonin Amirka 41 sun kasasnce a sahun farko na wadanda suka sayar da  kashi hamsin da hudu na cinikin makamai a duniya. Masana'antar Lockheed Martin ita kadanta ta sayar da makamai na sama da dala biliyan 58 a bara.

A nahiyar Turai kuwa, Faransa da Rasha sun sami koma baya a cinikin makamai, inda fadar mulki ta Moscow ta samu raguwar kashi  biyar kawai na jimilar makaman da aka sayar. A jimlance, kashi ashirin da daya cikin dari na makaman da aka sayar a duniya ne suka fito daga nahiyar Turai, inda a shekara ta 2020, kamfanoni ashirin da shida suka sayar da makamai na dala biliyan dari da tara. Kamfanonin kera makamai na  Jamus  guda hudu suka sayar da makamai na biliyan tara. 

Ita ma Simone Wisotzki  ta PRIF ta lura da cewa kamfanonin kera makamai daga kudancin duniya ma suna karuwa sosai, musamman a Indiya. Uku daga cikin kamfanonin kasar ne suka bayyana a cikin dari na farko da ke kare makamai, ma'ana suna siyar da  kashi 1.2 bisa dari na makaman a duniya, wanda ya yi daidai da adadin da  Koriya  ta Kudu ke siyarwa. Cibiyar ta SIPRI ta sanya Chaina a jerin kasashe da ke siyar da makamai, inda ta lissafa kamfanoni biyar da suka amfana da cinikin makamai, lamarin da ya kai kashi 13 cikin 100 na cinikin makamai na kanfanoni 100.