1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Karuwar safarar miyagun kwayoyi

April 18, 2023

Hukumomi a jihar Gaya ta Jamhuriyar Nijar sun nuna damuwa dagance da yadda safarar miyagun kwayoyi yake nema samun gurin zama

https://p.dw.com/p/4QG1F
Zentralafrikanische Republik AIDS-Medikament
Hoto: BARBARA DEBOUT/AFP/Getty Images

A tsakanin watanni uku jami'an tsaro na kan iyakoki da na ruwa sun yi nasarar kama kwoyoyin maye da yawan su ya haura nauyin kilogrammes 572. Kwamishinan yan sanda Saley Seini ya ce daga watan Janairu na shekarar 2023 zuwa 8 ga Watan Afrilu na 2023 sun yi nasarar kama kwoyoyin maye masu yawa da suka hada da tabar wiwi da hodar Iblis wato cocaïne, da Tramadol da dai sauran su. Sun kuma kama mutane 46 cikin su akwai yan Niger 35, yan kasar Bénin hudu, yan Nigeria hudu, dan kasar Mali daya, da yan kasar Togo biyu 

Jihar Gaya dai ta zama wata hanya da masu safarar miyagun kwayoyi ke bi domin shigar da kayansu. Gwamnar jihar Dosso ya mika kira ga jami'an tsaro domin kara zage damtse domin ci gaba da dakile masu neman shigowa da kwayoyin.

Daga nasa bangare shugaban karamar hukumar Gaya Hassimi Abarshi jinjina wa jami'an tsaro ya yi  bisa kokarin da suke ga yi. Jihar Gaya na cikin jihohin da matasa ke fama da shaye shayen miyagun kwayoyi da kuma safarar sa