Kasafin kudin Najeriya yayin da ake shirin zabe
December 7, 2018Sama da Tirilyan na nairar tarrayar najeriyar guda takwas ne dai Abuja ta ce tana shirin ta kasha a cikin kasafin dake zaman na karshe ga gwamnatin mai fuskantar zabe a badi.
A cikin makon mai zuwa ne dai ake sa ran mika daukacin kasafin ga majalisun kasar guda biyu da nufin tantancewa a cikin halin rikici a tsakanin shugabancin majalisar da ke jam'iyya ta adawa da kuma gwamnatin kasar mai mulki.
Kasafin da ke da fatan dorawa a bisa jeri na cigaban da gwamnatin ke ikirarin samu dai na zaman zakaran gwajin dafi ga gwamnatin da ke tsakanin burge 'yan kasar da sake samun zabe da kuma gazawa da kila fuskantar fushi na 'yan kasa.
To sai dai kuma bayan share tsawon awoyi kusan biyu yan majalisar zartarwar sunce basu da niyyar kara a cikin yanayi na kasar da nufin burge masu tunanin zabe a badi a fadar Hadi Sirika da ke zaman ministan harkokin sufurin sama kuma daya a cikin 'yan majalisar zartarwar.
A bara dai sai da ta kai kasar share tsawon watanni kusan bakwai tana jiran kasafin duk da kasancewar shugaban kasar da shugabannin majlaisun biyu daga jam'iyyar APC mai mulki.
Tsaka mai wuya cikin neman sauyi, ko kuma kokari na sauya da dama, in har masu gwamnatin suna shirin su fuskanci turjiya, can a cikin zauren majalisar dai bisa alamu kasafin na shirin samun sauki duk da tunani na siyasa a fadar Sanata Umar Kurfi da ke zaman dan majalisar dattawa daga Katsina.