Kasashen duniya za su karfafa tsaro a Somaliya
February 22, 2012A yau ne MDD za ta kada kuri'ar domin kara yawan dakarun kiyaye zaman lafiya a kasar Somaliya. Kungiyar Tarayyar Afirka wanda kawo yanzu dakarunta ne ke wanzar da zaman lafiya a Somaliya, tana bukatar a kara yawan dakarun daga 12000 izuwa dubu goma 17000. A barane dai dakarun kasashen Afirka dake Somaliya suka samu nasarar fatattakar mayakan Alshabab a aksarin babban birnin kasar da kuma wasu wurare dake kusa da birnin na Mogadishu. Batun kada kuri'ar da MDD za'a yi shine kwana guda kafin taron da kasashen duniya za su yi kan kasar ta Somaliya a birnin london. Manufar taron shine a kara shirin marawa gwamnatin rikon kwaryan kasar da a yanzu bata da cikkaken iko. Shugaban hukumar Tarayyar Turai wanda kuma itace tafi baiwa Somaliya tallafi mai soka, ya yi alkawarin cewa EU za ta kara agajin da take baiwa Somaliya. A halinda ake ciki kungiyar kare hakkin bil'adama ta HRW ta zargi zagerun Alshabab da yin amfani da yara kanana a matsayin soja.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu