1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Turai na sassauta dokar kulle

Abdullahi Tanko Bala
May 15, 2020

Jamus da sauran kasashen Turai da aka sami raguwar yaduwar cutar corona sun sassauta rufe iyakokinsu yayin da Mexico da sauran wurare basu kai ga ciwo kan annobar ba tukunna.

https://p.dw.com/p/3cHlm
Grenzkontrollen zwischen Deutschland und Österreich
Hoto: picture-alliance/picturedesk.com/F. Neumayr

Kasar Slovenia wadda sannu a hankali ta rage tarnaki kan dokar kulle, ta ce a yanzu ta dakile yaduwar cutar kuma 'yan kasashen Turai suna iya shiga kasar ta Austria da Italiya da kuma Hungary.

A halin da ake ciki Jamus na shirin bude iyakokinta da kasar Luxemburg a daren wannan Juma'ar kuma za ta bude wasu iyakokin da ke tsakaninta da kasashen Faransa da Switzerland da kuma Austria.

Sai dai kuma matafiya da ke son shiga Jamus sai sun nuna kwararan hujjoji na shiga kasar kuma za a rika gudanar da bincike. Jamus din dai na fatan dage tarnakin tafiye tafiye zuwa ranar 15 ga watan Juni.

Bugu da kari dukkan jihohin kasar sun amince su dakatar da bukatar matafiya daga tarayyar Turai killace kansu na kwanaki 14 idan suka shigo Jamus.

Gwamnan Jihar North Rhine-Westphalia Armin Laschet ya ce Jamus za ta shawo kan annobar corona ce idan aka sakar wa jama'a mara domin tafiye tafiye da kuma safarar kayayyaki.