EU: Rabin al'umma sun yi riga-kafin corona
August 31, 2021Talla
Wannan dai shi ne burin da kasashe mambobinn kungiyar ta Tarayyar Turai wato EU suka sanya a gaba tun a farkon wannan shekarar, inda suke fatan ganin ya zuwa yanzu sama da rabin alu'umma sun yi alurar.
A wani sakon bidiyo da ta wallafa a kafar internet, von der Leyen ta ce: "Mun cimma burinmu da ke da matukar muhimmanci a yaki da wannan cuta ta coronavirus, kaso 70 cikin 100 na alummarmu na da cikakkiyar kariya. Hakan na nufin sama da mutum miliyan 250, sun yi allurarsu duka."
Bullar nau'in Delta na zama babban kalubalen da duniya ke fuskanta a yanzu haka, lamarin da ya kai ga Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta nuna damuwa ga irin yawan wadanda cutar za ta halaka nan da zuwa karshen wannan shekara ta 2021 da muke ciki.