Kasuwancin China da Amirka na dagulewa
April 6, 2018Talla
Wannan dai na zuwa ne bayan da Shugaba Donald Trump ya yi barazana ta kara yawan haraji da ya kai dala miliyan dubu 100 a kayayyakin kasar ta China.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin kasuwanci a China Gao Feng ya bayyana cewa matakin da Amirka ke dauka babban kuskure ne da ke nuna babakeren kasar ta Amirka kuma bisa ga dukkan alamu ba za a samu maslaha tsakanin manyan kasashen biyu masu karfin tattalin arziki nan kusa ba.
Gao ya ce muddin Amirkar ta kara wa China harajin da ya kai dala miliyan dubu to ita ma ba za ta ji kunya ba wajen mayar da martani makamancin hakan kan kayan Amirka.