Karin watannin shida kafin rufe sansanin Dadaab
November 16, 2016Ministan cikin gidan kasar Kenyan Joseph Nkaissery ne ya bayyana hakan, abin da ya biyo bayan bukatar da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UN HCR ta shigar a kan wannan batu domin ganin an jinkirta rufe sansanin na Dadaab, sannan kuma ministan ya ce mayar da 'yan gudun hijirar kasashensu, zai wakana ne cikin mutunci da girmamawa nan da watanni shida masu zuwa a sabon wa'adin da gwamnatin ta dauka na kammala ayyukan rufe wannan babban sansani.
Sansanin na Dadaab da ke kusa da iyakar kasar ta Kenya da Somaliya, na dauke ne da 'yan gudun hijira akalla 280.000 wadanda akasarinsu 'yan kasar Somaliya ne da suka gudo tun daga shekara ta 1991, lokacin barkewar yakin basasa da kashe-kashen da masu kishin adini ke yi da kuma matsalar farin da suka tsinci kansu a ciki.