1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: An kulla kawancen yaki da zaman sojojin Faransa

Gazali Abdou Tasawa AMA(ZMA)
August 4, 2022

Kungiyoyin farar hula 15 sun kafa kawancen yaki da zaman sojojin Faransa a Nijar mai suna M62, tare da shirin tsara jerin tarukan gangamin kin jinin sojojin Faransa a Nijar.

https://p.dw.com/p/4F8iP
Frankreich Mali - Militär Konflikte
Hoto: Frederic Petry/Hans Lucas/picture alliance

Kawancen mai da’awar ‘yan kishin kasar Nijar da kare mutuncinta ya ce lokacin ya yi da ya kamata Nijar ta raba gari da kasar Faransa wacce suke zargi da yin katsalandan a harkokin cikin gida na kasar Nijar wanda suka ce na tauye duk kokarin da kasar take yi a samar da cikakken ‘yancin kanta. 

Kafa wannan sabon kawancen kungiyoyin yaki da zaman sojojin Faransa a Nijar na zuwa ne a daidai lokacin da Faransa ke ci gaba da jigilar sojojinta na rundunar Barkhane da kayan aikinsu kwantina dubu shida daga Mali zuwa kasar Nijar bayan raba gari da Malin. lamarin da sabon kawancen na M62 ya sha alwashin yin gwagwarmaya har sai sojojin Faransar sun fice daga kasar ta Nijar.

Karin Bayani: Za mu marabci sojin Turai a Nijar in ji Bazoum

Mali Frankreich beendet die Operation „Barkhane“
Rundunar Barkhane ta sojojin Faransa a Mali Hoto: AP Photo/picture alliance

Akwai wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam a Nijar da ke ganin duk wata mahawara kan wannan batu na zaman sojojin Faransa a Mali bakin alkalami ya rigaya ya bushe tun da har majalisar dokokin wacce ita ce doka ta bai wa wannan hurumi, ta amince da girke sojojin Faransar a Nijar. 

Abin jira a gani dai a nan gaba shi ne tasirin da kokowar da wannan sabon kawance na M62 za ta yi wajen ganin gwamnatin Nijar ta raba gari, kokowar da wasu kungiyoyin suka sha yi a shekarun bay aba tare da samun nasara ba.