Kokarin warware rikicin somaliya
November 26, 2006Kakakin majalisar dokokin gwamnatin Rikon kwarya na jeka nayika dake kasar Somaliya,ya rattaba hannu a yarjejeniyar zaman lafiya da gamayyar kungiyoyin musulmi dake da karfin madafan iko a sassa daban daban na kasar,ba tare da izinin gwamnatin ba.Tuni dai gwamnatin riko na Somaliyan tayi watsi da wannan yunkzri na Kakakin majalisa Sharif Hassan Sheikh Aden,inda tace bada yawunta ba.Ministan harkokin yada labarai na Somaliya Ali Ahmed Jama Jengeli,ya fadawa manema labaru cewa ,kakakin majalisar ya wuce kaidojin aikins,adangane da cimma yarjejeniya da yan adawan batare da samun izinin gwamnati ba.Shi kuwa a nashi Bangaren kakakin majakisa Sharif Aden cewa yayi,yana kokarin sasanta bangaren gwamnatin rikon wanda keda goyon bayan mdd,da bangaren kungiyoyin musulmin,wadanda sune keda akasarin madafan iko a kudancin kasar.