1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta daure tsohon minista a Zimbabuwe

Abdul-raheem Hassan
July 20, 2018

Samuel Undenge da ya taba rike mukamin ministan makamashi a gwamnatin Robert Mugabe ya shan dauri bayan da kotun Zimbabuwe ta sameshi da laifin cin hanci da karbar rashawa.

https://p.dw.com/p/31qRS
Simbabwe | ehemaliger Energieminster Samuel Undenge auf dem Weg zum Gerichtsgebäude von Harare
Hoto: Reuters/P. Bulawayo

Wata kotu a Zimbabuwe ta yanke wa tsohon ministan makamashin kasar hukuncin zaman shekaru hudu a kurkuku, bayan da ta sameshi da hannu a badakalar cin hanci a tsohuwar gwamnatin shugaba Robert Mugabe.

A yanzu tsohon ministan Samuel Undenge mai shekaru 62 da haihuwa zai shafe shekaru biyu da rabi a daure, bayan da ya yi shekara guda da rabi a kan zargi ba da kwangilar makudan kudade ta bayan fage.

Wannan dai shi ne karon farko da aka cimma nasarar daure wani daga cikin jiga-jigan jami'an tsohon shugaban kasar Mugabe. Gwamnatin shugaba Emmerson Mnangagwa ta yi aniyar sa kafar wando guda da ayyukan cin hanci da rasha, sai dai 'yan adawa na sukar tafiyar hawainiya a cika alkawarin yaki da cin hancin.