SiyasaJamus
Za a ci tarar kasar Poland bisa rashin dakatar da shirinta
October 27, 2021Talla
Kasar Poland ta jima ta na 'yar tsama da EU tun bayan da shugaban gwamnati Mateusz Morawiecki ya kudri anniyar kawo muhimman sauye-sauye a fannin kotun kolin kasar, lamarin da kuma kungiyar EU ta kira da rashin adalci da ma tauye cikakken 'yancin alkalai.
Ko farkon wannan watan ma sai da kotun tsarin mulkin Poland ta yi fatali da wasu kudirorin da suka shafi kungiyar ta tarayyar Turai, tana mai cewa sun yi hannun riga da kundin tsarin mulki.
Sai dai matakin kotun da kotun ta dauka a wannan Laraba, ya zo ne daidai da bukatar hakan da tun daga farko hukumar zartarwar EU din ta shigar, tana mai fatan ganin an dauki tsauraran matakai da ta kira na kare mutucin alkalan kotu.