SiyasaTurai
Kotun EU ta gano yadda Rasha ta yi kisan gilla
September 21, 2021Talla
Alexander Litvinenko ya rasu a shekara ta 2006 bayan kurbar wani shayi da aka barbada wa guba a Millennium Otel da ke Birtaniya. Kafin kisan gillar da aka yi ma sa, Litvinenko ya yi wa gwamnatin Rasha aikin samar da tsaro a hukumar tsaron kasar. Daga baya ne kuma tsohon jami'an ya koma Birtaniya ya rinka caccakar gwamnatin Rasha.
Sai dai hukumomin Rasha sun jima suna nesanta kan su da kisan gillar da aka yi wa Alexander Litvinenko wanda ya yi kaurin suna wurin kushe hukumar leken asirin Rashan.