1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

Kotun Turai ta yi fatali da yarjeniya da Maroko

Suleiman Babayo MAB
September 29, 2021

A wani hukunci da ka iya janyo sabani da Maroko, kotun Tarayyar Turai ta yi watsi da yarjejeniyar Tarayyar Turai kan shigar da kayayyakin Yammacin Sahara daga Maroko.

https://p.dw.com/p/413VX
Internationaler Protest I Free Sahara
Hoto: Fermin Rodriguez/NurPhoto/picture alliance

Kotun Tarayyyar Turai da ke birnin Brussels na kasar Beljiyam ta soke amincewar da mambobin kasashen 27 suka yi na shigar da kayyakin aikin gona da na albarkatun ruwa na yankin yammacin Sahara daga kasar Maroko. Ana ganin hukuncin kotu zai iya shafar sabanin dangantaka tsakanin kungiyar Tarayyar ta Turai da kasar Maroko, sai dai hukuncin kotun ya ce za a iya ci gaba da aikin da wasu bangarorin yarjejeniyar ta shekara ta 2019, bisa dalilan dokoki da huldar kasa da kasa.

Kungiyar Polisario mai fafutukar kwace 'yanci daga Maroko ta shigar da wannan kara a kotun ta Tarayyar Turai.