Taron EU: Dangantakar Tarayyar Turai da Turkiyya
December 10, 2020Shugabanin kasashen EU sun kira taron ne da zummar lalubo mafita daga matsalolin da ke adabar yankin dama kuma wadanda ke son haifar da rabuwar kanu a tsakaninsu. Taron da za a soma yi daga wannan Alhamis, zai mayar da hankali kan magance matsalar dumamar yanayi da yadda za a shawo kan rage hayakin da kasashen ke fitarwa. Sai kuma batun farfado da tattalin arzikin yankin da annobar corona ta ta'azzara da kuma dangantakar EU da Turkiyya da ake kace-nace kan iskar gas.
Mahalarta taron za su yi nazari kan harkokin cinikayya da Britaniya da ta raba gari da Tarayyar Turai. Firaiminista Boris Johnson zai halarci taron. Shugabanin za su ci gaba da tattauna yadda gwamnatocinsu za su tunkari aikin riga-kafin cutar corona a tsakanin kasashe mambobinta kafin sauran kasashen duniya. Wannan shi ne taro na farko da shugabanin kai yi bata kafar bidiyo ba, tun bayan bullar annobar Covid-19.