EU ta bukaci da a bude hanyoyin sadarwa a Tigray
December 4, 2020Biyo bayan toshe hanyoyin sadarwa da gwamnatin Habasha ta yi tun bayan fara tashin hankali a yankin Tigray, hukumar samar da zaman lafiya ta kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci da a bude hanyoyin sadarwar.
Haka zalika, hukumar ta bukaci da a tsagaita wuta ta bakin Janez Lenarcic da ke zama shugaban hukumar da ke samar da zaman lafiya ta EU, ya yin da ya kai wata ziyarar gani da ido a sansanin 'yan gudun hijira na Um-Raquba, inda ya tattauna da 'yan gudun hijirar Habashar da suka tsallake zuwa makwabciyar kasar ta Sudan.
Shugaban hukumar ya ce abin takaici da tausayi daga cikin ababen da ya tattauna da 'yan gudun hijirar, shine rashin sanin halin da danginsu da suka baro gida suke ciki sakamakon rashin hanyoyin sadarwa.
Kawo yanzu dubun dubatar 'yan gudun hijira daga Habasha ne suka tsallake zuwa gabacin Sudan.