1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kura ta fara lafawa a titunan birnin Ouagadougou

Salissou BoukariSeptember 18, 2015

Sannu a hankali al'ammurra sun fara lafawa a titunan birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, inda sojojin RSP masu juyin mulki suka takaita yawan sintirin da suke.

https://p.dw.com/p/1GYlh
Hoto: picture-alliance/dpa/L. Koula

Sai dai a wasu jihohin kasar rahotanni na cewa al'umma batayi biyayya ga dokar hana fitar dare da sojojin suka saka, inda ma sannu a hankali kungiyoyi daban-daban ke kokarin hada kai don nuna kin amincewarsu da juyin mulkin duk kuwa da tsatsauran matakan da sojojin suka dauka da farko. Janar Gilbert Diendéré wanda ya karbi ragamar mulkin kasar ta Burkina Faso bayan juyin mulkin, ya sanar da sakin Shugaban kasar na rikon kwarya Michel Kafando da wasu Ministocinsa biyu, amma kuma yace suna ci gaba da tsare Firaminista Yacouba Isaac Zida. A yau Jumma'a ne dai Janar Diendéré, zai gana da shugaban kasar Senegal, kuma shugaban kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO, kungiyar da tuni ta yi Allah wadai da wannan juyin mulki kamar sauran manyan kungiyoyi na duniya.