Kwanaki uku na makoki bayan harin Ouagadougou
January 16, 2016Manya da kananan makamai sojojin Burkina Faso suka yi amfani da su wajen kubutar da wadanda 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a hotal Splendid na Ouagadougou. Hasali ma mutane 150 ne suka yi nasarar cetowa da ransu a sumamen da suka kai bisa tallafin takwarorinsu na Faransa da kuma Amirka. Sannan an garzaya da 26 daga cikinsu asibiti sakamakon raunuka da suka samu. Sai dai kuma fito na fito da sassa biyu suka shafe tsawon lokaci suna yi, ya salwantar da rayukansu mutane 26 ciki kuwa da 'yan ta'adda hudu.
Kungiyar al- Murabitun da ke biyeyya ga Aqmi ta dauki alhakin wannan harin na Burkina Faso, wanda ya zo makonni kalilan bayan wanda ta kai a wani kasaitaccen hotal na Bamako babban birnin Mali. Har yanzu ba a kai ga tantance kasashen da wadanda harin na Ouagadougou ya ritsa da su suka fito ba. Sai dai hukumomin na Burkina Faso sun sanar da cewar sun fito ne daga kasashe daban-daban har 18.
Daya daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya a harin na babban birnin Burkina Faso ya ce da kyar sojojin kawance suka yi nasarar kubutar da su.
"Sun fara harbe-harbe da manyan bindigogi kafin 'yan bindingan biyu su kutsa cikin dakin da muke. Daya daga cikinsu ya harbeni a kafada. Sai dai wadanda suke daya gefen sun ji munanan raunuka. A wannan yanayi ne sojojin Faransa suka zo kubutar da mu. Sai dai a lokacin da muke fita daga hotal, 'yan bindigan sun sake far mana."
Faransa da Amirka sun taimaka wa Burkina Faso
Francois Hollande na Faransa, ya kasance shugaban farko da ya yi tir da harin ta'addanci da 'yan bindiga suka kai hotal Splendid na birnin Ouagadougou. Dama dai kasar tasa da ta yi wa Burkina Faso mulkin mallaka, ta rigaya ta jibge sojojinta a kusa da babban birni da nufin yakar masu kaifin kishin Islama da ke kai hare-hare a yankin Sahel. Ita ma Amirka da ke da dakaru 75 a Burkina Faso ta bayar da tata gudunmawa a fito na fito da sojojin kawance suka yi da wadanda suka kai hari tare da yin garkuwa da mutane a hotal Splendid. Kungiyar gamayyar Turai da kuma Ingila ma ba a barsu a baya ba wajen yin Allah wadai da abin da ya faru a Burkina Faso.
Cikin jawabin da ya yi wa manaima labaru, shugaban na Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore ya yaba irin gudunmawar da kasarsa ta samu daga kasashen ketare wajen murkushe wadanda 'yan ta'adda.
"Godiya ta tabbata ga dakarun kasa da kasa na Faransa da na Amirka, wadanda suka taimaka mana ganin haske a kokarin da muka yi na ganin bayan 'yan ta'adda. Za mu ci gaba da daukan matakan da suka dace. Amma muna kira ga 'yan Burkina Faso da su sa ido tare da kara kuzari saboda za mu sanya yaki da ta'addanci a tsarin rayuwarmu na yau da kullum."
Shugaba Kabore ya kuma yi kira ga kasashe makwabta da su hada gwiwa a fannin tsaro tare da musayar bayanan sirri wajen ganin bayan kungiyoyin ta'addanci a yankin yammacin Afirka.
Ko da shi ke dai wannan shi ne karon farko da kungiyar al-Murabitun da ke da alaka da Aqmi ta kai hari a Burkina Faso, amma kuma ta yi garkuwa da wani ma'aikaci dan kasar waje da ta yi garkuwa da shi a Arewacin Burkina Faso. A yanzu haka ma gwamnatin ta sanar da cewar 'yan ta'adda sun kame wasu 'yan Austriya biyu a Arewacin kasar.