A yayin da ake cikin fargaba da hana 'yan kallo shiga wasannin lig na kasashen Turai saboda tsoron sake dawowar annobar cutar coronavirus, shirin ya duba yadda lamarin yake a sauran sassan duniya da kuma sakamakon wasannin kwallon kafa na Bundesliga da Zakarun Turai na karshen makon jiya.