1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni 16.05.2022

Suleiman Babayo MA
May 16, 2022

A ciki za a ji bayanai kan wasanin lig-lig na kwallon kafar Jamus wato Bundesliga, inda a ranar Asabar kungiyoyi 18 na rukunin farko suka yi wasan kammala kakar Bundesliga.

https://p.dw.com/p/4BMqj
Bundesliga | FC Bayern München v VfB Stuttgart
Hoto: Michael Probst/AP/picture alliance

Tun farko dai ta tabbata cewa kungiyar Bayern Munich ta sake zama zakara, sannan a matsayi na biyu akwai Borussia Dortmund, kana a matsayi na uku akwai Bayer Leverkussen, inda Leipzig take matsayi na hudu. Yayin wasannin na karshen mako mun kawo muku sharhi kai tsaye na wasan da Stuttgart ta doke FC Kolon 2 da 1.

A wasannin La-Ligar Spaniya, kungiyoyin hudu da suka samu nasarar kai wa ga wasan zakaru na kasashen Turai da ake gani za su kammala lig na gaba sun hada da Real Madrid da Barcelona da Atletico Madrid da kuma Sevilla. A wannan makon ake kawo karshen wannan gasa ta La-Liga.

Spanien Fußball I Real Madrid feiert  Liga-Titel
Hoto: Bernat Armangue/AP/picture alliance

Daidai kuma lokacin da kasashen da suka samu nasarar tsallakewa zuwa gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a bana da kasar Katar za ta dauki nauyi, wani mataki kasashen irin Najeriya ya dace su dauka duk da cewa ba su samu shiga gasar ta bana ba, domin shirya wa gaba, Alhaji Sani Ahmed Toro, tsohon sakataren hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Najeriya kana tsohon kwamishinan wasanni a jihar Bauchi ya yi bayani. Sannan wani shiri kasashe musamman na Afirka da suka tsallaka zuwa gasar ta cin kofin duniya ya kamata su yi.

A wasannin Tenis, har yanzu Novak Djokovic dan kasar Sabiya, ya ci gaba da kasance gwani na gwanayen 'yan wasan a jerin da hukumar kula da wasan ta fitar, sannan a matsayi na biyu akwai Daniil Medvedev da kuma dan kasar Jamus, Alexander Zverev na matsayi na uku.