1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bayern Munich ta lashe kambun Bundesliga

Mouhamadou Awal Balarabe
April 25, 2022

Bayern Munich ta harbar tsuntsaye biyu da dutse daya, inda ta zama ta farko a Jamus da ta lashe kambun zakara na Bundesliga sau goma a jere, kuma ta farko a Turai da ke da wannan bajinta

https://p.dw.com/p/4AQIp
Lewandowski mit improvisierter Meisterschale
Hoto: Matthias Schrader/AP Photo/picture alliance

Yaya-babba Bayern Munich ta dora inda ta tsaya, inda ta sake zama zakaran kwallon kafar Jamus a ranar Asabar, bayan da ta doke abokiyar hamayyarta kuma Yaya-karama Borussia Dortmund da ci 3-1 a wasan mako na 31 na Bundesliga, lamarin da ya bata damar zama gwani na gwanaye karo na goma a jere. Dama dai Dortmund ta fuskanci kalubale na raunin 'yan wasan ciki har da golanta Gregor Kobel, lamarin da ya bai wa zaratan 'yan wasan Bayern damar cika burinsu, da kuma kwantar da hankalin koci koci Julian Nagelsman:

"Wannan ita ce babbar bajinta ta farko na rayuwata, don haka ya zama wani abu na musamman a gare ni. Matsayi ne da yake da ma'ana sosai a gare ni, bayan shekarar farko ta horo a Bayern Munich wanda a gaskiya ba abu ne mai sauki ba. Ba ni da wani mai korafi ba ne, amma akwai abubuwa da yawa da ba su gudana yadda ya kamata ba, kamar rashin nasara da har yanzu na kasa mantawa, Saboda haka ne nake farin cikin samun nasarar lashe wannan kambu."

Gasar Bundesliga | Bayern München da Borussia Dortmund
Hoto: Revierfoto/IMAGO

Wannan dai shi ne karo na 32 a tarihinta da Bayern Munich ta zama zakarar kwallon kafar Jamus, lamarin da ya sa ta yi wa takwarorinta zarra. Sannan ta zama ta farko a manyan lig na kasashen Turai da ta lashe kambun zakara sau goma a jere.

A sauran wasannin na mako na 31 kuwa, Union Berlin ta bi RB Leipzig har gida kuma ta doke da ci 2-1. nasarar da ke bai wa Union damar zama ta 6 a teburin Bundesliga, kuma tana kwanton tikitin shiga gasannin kwallon kafa na Turai. A halin yanzu dai, Leverkusen na matsayi na 3, bayan nasarar da ta yi a kan 'yar baya ga dangi Greuther Fürth da ci 4-1. A yanzu dai ta tabbata a hukumance cewa  Greuther Fürth ta koma mataki na biyu na Bundesliga shekara daya kacal da shiga cikin manyan masu fafutuka a babban lig kwallon kafar Jamus. Yayin da Arminia Bielefeld wacce Cologne ta lallasa da ci 3-1, ta makale a matsayi na 17 amma har yanzu ba a san makomarta ba tun da akwai ratar maki biyu kacal da Stuttgart. 

VfL Wolfsburg  da FSV Mainz 05
Hoto: Swen Pförtner/dpa/picture alliance

Ita kuwa Wolfsburg ta yi wa Mainz kaca-kaca ci 5-0, yayin da FC Augsburg ta doke Bochum da ci 2-0, su kuwa Frankfurt da Hoffenheim suka tashi ci 2-2.

A daidai lokacin da ya rage sa'o'i 24 a fafata wasan daf da na karshe a gasar cin kofin zakarun kwallon kafa na nahiyar Turai, ta tabbata dai cewa fitattun 'yan wasa kimanin goma da ke da tushe da Afirka ne za su bada gudunmawa a cikin wadannan fitattun kungiyoyi. Alalhakika ma dai akasarin 'yan kwallon irin su su Sadio Mane ko mohamed saleh sune kashin bayan kungiyoyinsu, lamarin da magoya bayansu a Najeriya ke ganin cewa za suyi tasiri wajen nasara a gasar, kamar yadda za ku ji cikin wannan rajoton da Wakilinmu a Bauchi Aliyu Muhammad waziri ya aiko mana.