Kungiyar EU na son a samar da gwamnati a Lebanon
June 19, 2021Talla
Babban jami'in harkokin kasashen ketare na kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya yi kira ga shugabannin siyasar kasar Lebanon da su hanzarta samar da gwamnati a kasar da ke fama da matsin tattalin arziki.
A cewar babban jami'in ba za su iya bada wata gudumawa ba idan ba a tsaida gwamnati ba dama yin gyare-gyare a harkokin gudanar da kasar.
Ya yi wannan jawabin ne jim kadan bayan tattaunawa da shugaban kasar ta lebanon Michel Aoun, inda ya ce shirye suke su taimaka amma sai an fara tafiyar da gwamnati yadda ya kamata.
Kasar dai na cikin matsanancin tattalin arzki wanda ya sanyata shiga yanayi na bukatar taimakon gagawa, amma rashin kafa gwamnati tun a shekarar da ta gabata na neman ya janyo musu tsaiko a samun taimakon da ya kamata.