1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace-mace a hari kan 'yan sanda a Somaliya

Mouhamadou Awal Balarabe
December 14, 2017

Mutane akalla goma sun rigamu gidan gaskiya yayin da dama suka jikata lokacin da aka kai wa jami'an 'yan sanda harin kunar bakin wake a Mogadishu babbaan birnin Somaliya.

https://p.dw.com/p/2pLSH
Somalia Mogadishu Bombenexplosion
Hoto: Reuters/F. Omar

Wani dan kunar bakin wake ya tada bam da ke daure a jikansa a babbar cibiyar horas da 'yan sanda na Mogadishu babban birnin kasar Somaliya a safiyar Alhamis, inda mutane da dama suka rasa rayukansu. Shaidu sun nunar da cewar a daidai lokacin da 'yan sanda ke shirin yin atisayensu na safe ne dan takifen sanye da kayan sarki ya kai wannan hari harin.  Rundunar 'yan sandan Somaliya ta ce jami'an jinya na ci gaba da aikin fitar da wadanda suka mutu da wadanda suka jikata.

 Babu dai wata kungiyya da ta dauki alhakin kai harin. Sai dai kungiyar al Shabaab mai alaka da Al-Qaeda ta saba kai farmaki a kan 'yan sanda tun shekaru goma da suka gabata da nufin hambarar da gwamnatocin Somaliya da ke da goyon bayan kasashen duniya. Kungiyar al Shabaab ta rasa iko da Mogdishu a shekara ta 2011, amma tana ci gaba da kaddamar da hare-hare a kan sojoji da jami'an gwamnati da fararen hula a babban birnin kasar da kuma sauran wurare.