Mace-macen Coronavirus a China ya kai 1500
February 14, 2020Talla
Daga cikin karin mutane 116 da suka rasu 88 daga cikinsu suna lardin Wuhan ne inda aka fara samun bullar kwayar cutar a bara.
Hukumar lafiyar ta ce an sabbin kamun cutar har mutum 4,823 a Hubei wanda ya kai adadin wadanda ke dauke da kwayar cutar a lardin zuwa 55, 748
Karin adadin na zuwa ne bayan mutuwar mutane 242 da kuma sabbin kamu 14,000 kawo yanzu kwayar cutar ta Coronavirus ta yadu a kasashe 27 bayan China.
Ministan lafiya na Jamus Jens Spahn ya shaidawa tashar DW cewa ana cigaba da kokari na gano cutar da kuma daukar matakan dakile ita a tsakanin kasashen Turai. Ya jaddada bukatar hada hannu domin ganin cutar bata zama babbar annoba a duniya baki daya ba.