Faransa ya bukaci adalci a rabon yan cirani
September 19, 2019Talla
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Firaministan Italiya Giuseppe Conte sun yi wannan kiran ne a ranar Laraba yayin da suke kokarin sasantawa kan tsamin dangantakar da aka samu a tsakanin kasashen biyu a karkashin gwamnatin Italiya da ta gabata mai akidar kyamar baki.
Kasar Italiya dai ta sha yin korafi cewa sauran kasashen Turai ba sa daukar nauyin da ya dace na dubban daruruwan 'yan gudun hijira da suka isa gabar ruwan Italiya a 'yan shekarun baya bayan nan.