1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maganin gargajiya na warkar da maleriya

Zainab Mohammed Abubakar MAB
March 15, 2019

Hukumar lafiya ta duniya ta ruwaito cewar mutane miliyan 212 sun kamu da maleriya  a shekarar 2015, a yayin da dubu 429 suka rasa rayukansu. To ya tasirin amfani da ganyaye da itatuwa a matsayin hanyar yakar maleriya?

https://p.dw.com/p/3F6jz
Malaria Senegal
Hoto: DW/E. Landais

Duk da cewar ra'ayoyi sun zo guda dangane da bukatar kawar da zazzabin cizon sauro, ra'ayi sun banbanta a duniyar kwararru a fannin kiwon lafiya dangane da hanyoyin da za a iya cimma wannan buri. A yanzu haka dai wasu itatuwa da aka samu a kasar Chaina sun fara sauya lamura, inda kwararru suka nunar da cewar, a kan sauya ganyen itacen zuwa ganyen shayi .

Wata kungiyar masana a fannin kimiyya ta kasa da kasa da wasu likitocin da aka alakanta da kungiyar La Maison, sun dauki shekaru masu yawa suna gwajin tasirin wannan itaciya a matsayin maganin yakar cutar zazzabin cizon sauro wato maleriya.

Kasashen Afirka na fama da matsalar amfani da magani fiye da kima wajen kokarin warkar da zazzabin cizon sauro, duk kuwa da yawan gwaje- gwaje. Magunguna kamar Chloroquine da Sulfadoxine hade da Pyrimethamine da Quinine dai, sanannun magungunan maleriya ne a Afirka. Sai dai Kuma amfani da su fiye da kima ya sanya wasu daga cikinsu bijirewa cutar, wanda ya tilasta neman wata mafiyar idan har ana muradin kawar da cutar. 

Malaria Senegal
Maganin gargajiya na amfani wajen yakar maleriya a Senegal Hoto: DW/E. Landais

Tun daga shekara ta 2000 dai an samu raguwar mace-mace daga cutar maleriya a duniya baki daya. A kasar Senegal alal misali, akwai mutane kasa da dubu 300 da ke fama da malaria, idan aka kwatanta da dubu 700 shekaru 10 da suka gabata. Dr Alioune Gueye na cibiyar yaki da cutar maleriya ta kasa ya danganta nasarar da tsarin kula da lafiya na Senegal da rarraba magunguna da gidan sauro kyauta...

Sai dai ya nuna shakku dangane da amincewa da itacen Artemisia, a matsayin maganin waraka daga zazzabin na cizon sauro, ba tare da kara gudanar da bincike kan maganin ba. Bincike ya nunar da cewar, busashen ganyen itacen Artemisia ya warkar da mutane  da dama daga zazzabin cizon sauro a kasar Kwango da Amirka a shekara ta 2017, inda ta hanyar shansa a matsayin shayi, mutane 18 da ke fama da maleriya suka samu waraka.