1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin mayakan jihadi a Burkina Faso

Zainab Mohammed Abubakar
February 2, 2020

Wasu da ake zargi da kasancewa mayakan jihadi sun kashe fararen hula wajen 20, a wani hari da suka kai a kauyen Bani da ke gunduwar Seno a yankin arewacin kasar Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/3XAQ4
Symbolbilder Niger Armee
Hoto: picture-alliance/Zumapress/D. White

Rahotanni na nuni da cewar, maharan dauke da manyan makamai akan babubura, sun yi harbin kan mai uwa da wabi kan fararen hula a daren jiya, kafin su fice daga kauyen.

Wani jami'in kula da lafiya a garin Dori da ke makwabtaka, ya shaidar dacewar, babbar jami'ar kula da lafiya a kauyen na daga cikin mutane 20 da maharan suka kashe.

Kididdigar MDD na nuni da cewa, a shekara ta 2019 wajen mutane 4,000 suka rasa rayukansu daga harin mayakan jihadin a kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso, a yayin da aka tilasta sama da dubu 600 tserewa daga matsugunensu.