An kashe fararen hula 51 a arewacin Mali
August 9, 2021Talla
Wannan ya tayar da hankalin mahukunta kan tsanantar tashe-tashen hankula a wannan yanki na sahel.
Maharan dai sun afkawa kauyuka uku da ke kan iyakar Mali da Nijar a ranar Lahadi, inda suka kashe dukkan mazauna kauyukan na Karou da Ouatagouna da Daoutegeft.
Maharan kazalika sun lalata gidaje bayan dibar ganima na kaya da shanu da wasu dabbobi. Rahotanni na nuni da cewar, maharan sun zo ne cikin ayari a kan babura dauke da bindigogi.