1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahawara kan 'yan sandan jihohi

Uwais Abubakar Idris
July 13, 2018

A Najeriya majalisar datawan kasar ta fara muhawara a kan kudurin dokar da ke bukatar samar da ‘yan sanda na jihohi bayan kwashe shekaru ana fafatawa a kan wannan batu mai sarkakiya.

https://p.dw.com/p/31PYv
Symbolbild Nigeria Polizei
Hoto: imago/Xinhua

Gazawa ko raguwar tasirin da jami’an ‘yan sandan da ake da su a Najeriyar ne dai ya fara dago wannan batu na bukatar samar da ‘yan sanda na jihohin, lamarin da ya kai ga matsin lamba biyo bayan yawaitar munanan kasha-kashen da ake fuskanta a kasar. Alamu na a zahiri lalacewar rashin tsaro da ta kai ga babu birni ba kauye, kisan jama’a da sace su ne kawai ake yi ba tare da hukunta masu laifi ba.

Majalisar da ta ba da kai bori ya hau a kan wannan batu, ta kai ga gabatar da kuduri a karkashin mataimakin shugaban majalisar Sanata Ike Ekweremadu da ya bayyana fata ta kai wa ga amincewa da kuduri. To sai dai tun kafin a yi nisa da alamun ra’ayoyin ‘yan majalisar ya sha bamban a kan wannan batu, doming a Sanata Kabiru Marafa daga jihar Zamfara, inda ake fama da kashe-kashe ya ce akwai fa gayra a batun.

Za’a sa ido a ga irin fafatawar da za’a yi a kan wannan kuduri da a fili wani bangaren Najeriyar ke kan gaba wajen dage wa a samar da shi, a yanayin da ake fama da yadda za’a yi da jami’an sa kai na ‘yan banga irin na Peace Corp da shugaba Buhari ya ki sanya hannu a dokar halarta su.