1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Somaliya ta zaɓi shugaba

August 28, 2012

Wakilan majalisar sun zaɓi Mohamed Osman Jawari a kan muƙamin tsohon minista a tsohuwar gwamnatin Siad Barre wanda aka kiffar a shekara ta 1991

https://p.dw.com/p/15yyZ
Somali President Sheikh Sharif Sheikh Ahmed arrives to mark the first year anniversary since the ouster of militant Al Shabaab fighters from the capital Mogadishu August 6, 2012. REUTERS/Omar Faruk (SOMALIA - Tags: CIVIL UNREST POLITICS ANNIVERSARY)
Hoto: Reuters

Jawari bai taɓa riƙe wani matsayi na siyasa ba, tun daga lokacin, i'n banda , a baya baya nan da ya jagorancin kwamitin da ya girka sabbin dokokin tsarin mulki na ƙasar.zaɓen wanda shi nne mataki na farko na girka sabbin hukumomin ga ƙasar wacce marabinta da cikkakiyar gwamnatin tun shekaru 21 da suka gabata:

Zai kasance jagora ga wani zaman da majalisar zata yi a makon gobe, domin zaɓen shugaban ƙasar. Wanda kuma shi ne lamari mafi ɗaukar hankali da ƙasahen duniya masu bai wa ƙasar tallafi ke jiran ganin an aiwatar.Yan takara guda shidda ne , zasu fafata a ciki hadda tsofin fraministoci guda biyu Hassan Abshir da kuma Ali Khalif dukanin su yan ƙabilar darod ,ƙabila mafi rinjaye a ƙasar ta Somaliya.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi