Jagoran adawa a Rasha ya samu lambar yabo
October 20, 2021Talla
Mai shekaru 45 da haihuwa kuma mutumin da ya tsallake rijiya da baya, bayan saka masa guba a watan Augustan 2020 Navalny, yana zaman gidan yari na shekareuu biyu da rabi.
Kasashen EU dai sun kakaba wa Rasha takunkumi dangane da sanya wa jagoran adawar guba da kuma tsare shi da ta yi. Kungiyar 'yan majalisa mafi girma ta tarayyar Turai da ake kira EPP Group ce ta sanar da bashi lambar yabon a shafinta na Twitter, saboda fafutukarsa wajen kalubalantar shugaban Rasha Vladimir Putin.